INEC ta haramta wa masu zabe amfani da wayar salula yayin kada kuri’a a rumfar zabe

0
95

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ba za ta bari masu kada kuri’a su yi amfani da wayoyinsu na hannu ba a lokacin kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa da za a yi ranar Asabar.

Kwamishinan zabe na jihar Ogun, Niyi Ijalaye ne ya bayyana hakan jiya a Abeokuta yayin wata tattaunawa da manema labarai bayan wata ganawa da shugabannin hukumomin tsaro gabanin zaben na ranar Asabar.

Ijalaye ya ce, laifi ne ga masu kada kuri’a yin amfani da wayoyinsu na hannu a rumfunan zabe, ya jaddada cewa, wannan tsarin na daga cikin matakan da za a bi wajen hana sayen kuri’u a lokacin zabe.

Kwamishinan ya bayyana cewa ba za a bari masu kada kuri’a su amsa ko su kira waya ba, ko daukar hotuna da wayoyinsu a lokacin da suke kada kuri’a, ya kuma bayyana shirin hukumar zabe na gudanar da sahihin zabe tare da taimakon jami’an tsaro da hukumomi daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here