Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NAFDAC ta ce daga shekarar 2024 za a daina sayar da giya ‘yar leda ko ta karamar kwalaba saboda bazata sabunta lasisin masu yin taba.
Babbar daraktan hukumar farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana haka a Legas.
Ta ce hukumar zata tabbatar wa’adin lasisin bai zarta shekarar 2024 ba.
“ ko dayake muna fama da illolin da cutar korona ta haifar mana, NAFDAC na nan kan bakarta na aiwatar da dukkan ka’idoji da sharruda na kiyaye lafiyar ‘yan Najeriya musamman matasa wadanda sune sukafi cutuwa.
Dama dai masu Samar da giyar ‘yar leda sun amince su rage adadin da suke samarwa da kaso 50 cikin 100 a wani mataki na daina Samar da ita nan da shekarar 2024.