Champions League: Abin da ya kamata ku sani kan wasannin Talata

0
135

Za a ci gaba da wasanni na biyu a cikin rukuni a Champions League, inda za a kara a fafatawa bakwai ranar Talata.

Rukuni na daya da na biyu da na uku da kuma na hudu ne za su buga wasa na bibiyu.

Mohammed Abdu ya hada rahoto kan wasannin Champions League bakwai da za a yi ranar Talata.

Rukunin farko

  • Ajax Amsterdam
  • Napoli
  • Liverpool
  • Glasgow Rangers

Liverpool da Ajax Amsterdam

Liverpool da Ajax sun kara sau hudu a Gasar Zakarun Turai, inda Liverpool ta ci wasa biyu, Ajax ta yi nasara daya da canjaras daya.

Jerin haduwar da suka yi:   

2020/2021

Champions League Talata 1 ga Disambar 2020

  • Liverpool         1 – 0     Ajax

Champions League Laraba 21 ga watan Oktoban 2020

  • Ajax     0 – 1     Liverpool

1966/1967

European Cup Laraba 14 ga watan Disambar 1966

  • Liverpool         2 – 2     Ajax

European Cup          We 07Dec 1966

  • Ajax     5 – 1     Liverpool

To sai dai mai tsaron bayan Liverpool, Andy Robertson ba zai buga wasan na ranar Talata da Ajax ba, bayan raunin da ya ji.

Ana sa ran sai cikin watan Oktoba dan kwallon tawagar Scotland zai koma taka leda.

‘Yan wasan tsakiya na Liverpool da ke jinya sun hada da Curtis Jones da Naby Keita da kuma Alex Oxlade-Chamberlain.

Dan wasan Ajax daya ne ke jinya shi ne dan kwallon tawagar Netherlands mai tsaron baya daga gefen hagu, Owen Wijndal.

Tuni kuma aka dage daya wasan da ya kamata Rangers ta karbi bakuncin Napoli ranar Talata an mayar da shi zuwa Laraba.

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta ce hakan ya zama wajibi, domin za a samu karancin jami’an tsaro, bayan da ake makokin rasuwar Queen Elizabeth II.

UEFA ta kara da cewar ”ba ta amince ‘yan kallon Napoli su ziyarci gidan Rangers ba ranar Laraba, haka kuma magoya bayan Rangers ba za su je Italiya ba a wasa na biyu ranar 26 ga watan Oktoba”.

Rangers ta yi rashin nasara a gidan Ajax da ci 4-0 a makon jiya a wasan farko a cikin rukunin farko, ita kuwa Napoli ta caskara Liverpool 4-1 a daya wasan rukunin.

An dage dukkan wasannin Scotland a karshen mako, domin zaman makokin rasuwar Sarauniya.

Sakamakon wasan farko:

  • SSC Napoli 4 : 1 Liverpool
  • Ajax Amsterdam 4 : 0 Glasgow Rangers

Rukuni na biyu

Atletico Madrid

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

  • Atletico de Madrid
  • Club Brugge
  • FC Porto
  • Bayer 04 Leverkusen

A rukuni na biyun za a fafata tsakanin Bayer 04 Leverkusen da Atletico Madrid.

Sau takwas suka kece raina a tsakaninsu, Atletico ta ci uku, Leverkusen ta yi nasara a biyu da canjaras uku.

Jerin wasannin da suka kara:

2019/2020

Champions League Laraba 6 ga watan Nuwambar 2019

  • B Leverkusen  2 – 1     Atl Madrid

Champions League Talata 22 ga watan Oktoban 2019

  • Atl Madrid       1 – 0     B Leverkusen

2016/2017

Champions League Laraba 15 ga watan Maris 2017

  • Atl Madrid       0 – 0     B Leverkusen

Champions League Talata 21 ga watan Fabrairun 2017

  • B Leverkusen  2 – 4     Atl Madrid

2014/2015

Champions League Talata 17 ga watan Maris 2015

  • Atl Madrid       1 – 0     B Leverkusen

Champions League Laraba 25 ga watan Fabrairun 2015

  • B Leverkusen  1 – 0     Atl Madrid

2010/2011

Europa League  Alhamis 16 ga watan Disambar 2010

  • B Leverkusen  1 – 1     Atl Madrid

Europa League Alhamis 30 ga watan Satumbar 2010

  • Atl Madrid       1 – 1     B Leverkusen

Haka kuma a rukunin na uku FC Porto za ta karbi bakuncin Club Brugge.

Porto da Club Brugge sun yi wasa hudu a tsakaninsu, inda Porto ta yi nasara a uku, Brugge ta ci daya.

Wasannin da suka kara a tsakaninsu:

2016/2017

Champions League Laraba 2 ga watan Nuwambar 2016

  • Porto   1 – 0     Club Brugge

Champions League Talata 18 ga watan Oktoban 2016

  • Club Brugge    1 – 2     Porto

1972/1973

UEFA CUP Laraba 8 ga watan Nuwambar 1972

  • Club Brugge    3 – 2     Porto

UEFA CUP Laraba 25 ga watan Oktoban 1972

  • Porto   3 – 0     Club Brugge

Sakamakon wasan farko:

  • Atletico Madrid 2 : 1 FC Porto
  • Club Brugge 1 : 0 Bayer 04 Leverkusen

Rukuni na uku

Bayern Barca

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

  • Barcelona
  • Bayern Munich
  • Inter Milano
  • FC Viktoria Plzen

Za a fafata tsakanin FC Bayern Munich da Barcelona

Kungoyin sun fuskanci Juna sau 13 a Gasar Zakarun Turai, inda Bayern ta ci tara, Barcelona ta yi nasara a biyu da canjaras biyu.

Jerin karawar da suka yi a tsakaninsu

2021/2022

Champions League Laraba 8 ga Disambar 2021

  • B Munich         3 – 0     Barcelona

Champions League Talata 14 ga watan Satumbar 2021

  • Barcelona        0 – 3     B Munich

2019/2020

Champions League Juma’a 14 ga watan Agustan 2020

Barcelona        2 – 8     B Munich

2014/2015

Champions League Talata 12 ga watan Mayun 2015

  • B Munich         3 – 2     Barcelona

Champions League Laraba 6 ga watan Mayun 2015

  • Barcelona        3 – 0     B Munich

2012/2013

Champions League Laraba 1 ga watan Mayun 2013

  • Barcelona        0 – 3     B Munich

Champions League Talata 23 ga watan  Afirilun 2013

  • B Munich         4 – 0     Barcelona

2008/2009

Champions League Talata 14 ga watan Afirilun 2009

  • B Munich         1 – 1     Barcelona

Champions League  Laraba 8 ga watan Afirilun 2009

  • Barcelona        4 – 0     B Munich

1998/1999

Champions League Laraba 4 ga watan Nuwambar 1998

  • Barcelona        1 – 2     B Munich

Champions League Laraba 21 ga watan Oktoban 1998

  • B Munich         1 – 0     Barcelona

1995/1996

UEFA CUP Talata 16 ga watan Afirilun 1996

  • Barcelona        1 – 2     B Munich

UEFA CUP Talata 2 ga watan Afirilun 1996

  • B Munich         2 – 2     Barcelona

Daya wasan na rukuni na ukun za a yi ne tsakanin FC Viktoria Plzen da Inter Milan.

Wannan shi ne karon farko da za su kara tsakanin Viktoria Plzen da Inter Milan.

Sakamakon wasan farko:

  • Inter Milan 0 : 2 FC Bayern Munich
  • FC Barcelona 5 : 1 FC Viktoria Plzen

Rukuni na hudu

Tottenham

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

  • Sporting CP
  • Tottenham
  • Olympique Marseille
  • Eintracht Frankfurt

Za a kai ruwa rana tsakanin Sporting da Tottenham

Sporting da Tottenham ba su taba fuskantar juna ba a Gasar Kofin Zakarun Turai.

Daya wasan shi ne tsakanin Olympique Marseille da Eintracht Frankfurt.

Wannan ne karo na uku da za su kece raini a tsakaninsu, inda Frankfurt ta ci dukkan haduwa biyu baya.

Wasannin da suka yi a tsakaninsu:

2018/2019

European League Alhamis 29 ga watan Nuwambar 2018

  • E Frankfurt      4 – 0     Marseille

European League  Alhamis 20 ga watan Satumbar 2018

  • Marseille         1 – 2     E Frankfurt

Sakamakon wasan farko:

  • Eintracht Frankfurt 0 : 3 Sporting
  • Tottenham 2-0 Olympique Marseille