Masu sana’ar sinima sun yi cinikin Naira miliyan 378 a Agusta a Nijeriya

0
124
Kungiyar masu Haska Fina-finai. Silima ta Najeriya, CEAN, a yau Talata ta ce ta samu Naira miliyan 378 daga tikitin da aka sayar a gidajen silima na kasar nan a watan Agusta kaɗai.
Ope Ajayi, shugaban CEAN na kasa ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN.
Ajayi ya ce adadin ya nuna ƙaruwar kashi 28 cikin dari idan aka kwatanta da Naira miliyan 294 da aka samu a watan Agustan 2021.
Sai dai ya ce an samu raguwar cinikin tikiti da aka sayar da kashi 19 cikin 100 a watan Agusta, saboda cinikin Naira miliyan 471 a ka yi a watan Yuli.
“Fina-finanai 37 da aka nuna a watan Agusta sun samu sama da Naira miliyan 378 a ofishin akwatin.
“Fina-finan Hollywood 13 sun kai kashi 72.4 cikin dari, yayin da fina-finan Nollywood 16 suka yi kadan sama da kashi 22 cikin dari,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here