Gwamnatin Kano ta ware samada naira miliyan 300 domin biyan alawus na malaman jami’ar Jihar

0
100

Majalisar zartarwar Jihar Kano ta amince da sakin kudi fiye da naira miliyan 300 ga maaikatar ilimi mai zurfi don biyan alawus na malaman jamiar Yusuf maitama Sule su 287.

Kwamishinan yada labarai na Kano comrade Muhammad Garba ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai game da zaman majalisar zartarwa daya gudana.

Malam Muhammad Garba ya ce biyan kudin zaayi ne kashi kashi wanda zai fara daga watan oktoba.

Ya kara da cewa majalisar ta kuma amince da sakin fiye da naira miliyan 82 domin sayen kayan aiki ga fannin ilimin kimiyya na jamiar wanda ya hada da kujeru da tebura na ofishin malamai da dakin gwaje gwaje.

Ya kara da bayyana cewa majalisar ta kuma da baiwa jamiar kimiyya da fasaha ta Wudil fiye da naira miliyan 84 don biyan alawus na koyarwa na shekarar 2019 zuwa 2020 Sai kuma 2021 zuwa 2022.