Ginin Mai hawa hudu Wanda ya rushe a kan titin Akah a cikin babban birnin jihar har zuwa yanzu ba’a iya tantace yawan mutanan da ginin ya danne ba ko suka makale.
Daraktan hukumar Bada agajin gaggawa Dake kula da kudu maso kudancin Najeriya Mr Godwin Tepikor ya tabbatarwa da manema labarai cewa daga karfe 7 na yammacin yau Asabar zuwa karfe 9 na dare sun ceto mutane 5 .