Mahaifiyar tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu ta rasu

0
94

Mahaifiyar tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kasa EFCC Ibrahim Magu Hajja Bintu Jamarema ta rasu.

Hajja Bintu Mai shekara 92 a duniya ta rasu ne bayan Yar gajeruwar rashin Lafiya .

A sakon da ya aike a shafinsa na Tuwita Ibrahim Magu yace Innallihi wa Inna ilaihi raijun ,na rasa mahaifita a wani asibti Dake birnin Maiduguri a jihar Borno .

Yace tuni akayi janaizarta ta birnin Maiduguri.

Yayi fatan Allah yaji kanta da sauran musulmai.