DA ƊUMI-ƊUMI: Dalibai sun tare filin jirgin sama na Legas bisa zanga-zangar yajin aikin ASUU

0
96

Ɗalibai, ƙarƙashin ƙungiyar dalibai ta kasa, NANS, ta rufe hanyoyin da ke zuwa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas.

Ci gaban zanga-zangar wani mataki ne na nuna adawa da matakin yajin aiki da kungiyar malaman jami’o’i ke yi.

Duk da mamakon ruwan saman da a ke yi, ɗaliban sun jure sun fito, inda su ka haifar da cunkoson ababen-hawa a titin da ke kan hanyar zuwa filin jirgin, lamarin da ya sa matafiya da dama suka makale.

Jaridar The Nation ta lura da jami’an rundunar ƴan sandan jihar Legas, da jami’an RRS, da na ‘yan sandan filin jirgin saman Legas, da sauran jami’an tsaro suna nan a wajen.

Ɗaliban da suka gudanar da zanga-zangar na dauke da alluna da kwalaye, su na ta rera wakokin gwagwarmaya domin nuna rashin jin dadinsu kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.

 

(Daily Nigeria)