Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa naira tiriliyan 42

0
61

Yawan bashin da gwamnatin Najeriya ta ciyo ya karu zuwa Naira tiriliyan 42.

Ofishin Kula Basuka na Kasa ya ce a cikin wata uku daga Maris zuwa Yunin bana Najeriya ta ciyo karin bashin Dala biliyan uku, wanda ya sa abin da ake bin ta karuwa zuwa Dala biliyan 103.31 daga Dala biliyan 100.

Hakan na nufin idan aka raba wa ’yan Najeriya mutum miliyan 200 bashin, kowanne zai biya Naira 210,000.

Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce “Basukan da ake bin kasar nan sun karu ne saboda rancen da Gwamnatin Tarayya ta karba domin cike gibin da aka samu a kasafin 2022 da kuma basukan da gwamnatocin jihohi da Birnin Tarayya suka ciyo,” a cikin wata ukun.