Shugaban rukunin Kamfanonin man fetur na kasa NNPC Mele Kyari yace yanzu jihohin Oyo da Ogun sunfi sauran jihohin Najeriya amfani da Man Fetur.
Mele Kyari yace gwamnatin tarayya ta gano cewa anfi afani da Man Fetur din ne a jihohin guda biyu saboda suna makotaka da kasashen waje .
Yace gwamnatin tarayya tana kashe sama da naira tirilyan 3 da miliyan dubu 4 domin biyan kudin tallafin man fetur ga duk Litar man fetur miliyan 66 da dubu dari 7.
Yace hakan Yana daga cikin dokar albarkatun man fetur da akayiwa gyara ta shekarar 2022.
Yace abinda jihohin guda biyu suke amfani dashi na yawan man fetur ya rubanya abinda Lagos take amfani dashi
Mele Kyari wanda babban jami’in kula da hada Hadar kudi na Kamfanonin NNPC Umar Ajia ya wakilta yayi wannan tsokacin ne a gaban kwamitin hadin guiwa Mai bibiyar yadda aka kashe kudin tallafin man fetur daga shekarar 2013 zuwa 2021.