’Yan Sanda sun kama wata mata da yara tara da ta dauko

0
104

Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta kama wata mata a jihar da ta dauko yara tara a motar daukar kaya, daga karamar hukumar Danbatta da ke Kano, ta nufi zuwa jihar Ogun da su.

Yaran dai sun hada da masu shekaru 10 zuwa 15, kuma matar ta nufi garin Ijebu-Ode da je jihar Ogun ne da su, kafin a tare ta a jihar ta Kaduna.

Kakakin rundunar a Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce sun tare motar ce a shingen bincike na Kurmin Mashi, bayan sun lura babu taga ko daya a jikinta, duk da cewa akwai mutane a ciki.

Ya ce za su ci gaba da bincike kan lamarin, kafin daukar mataki na gaba.