Za’a gurfanar da makashin Ummita a kotu ranar Laraba

0
196

A ranar Laraba 21 ga watan Satumba 2022 ne a ake saran gurfanar da Ɗan ƙasar Chainan nan mai suna Ghen Quanrong da ya hallaka wata matashiya Ummulkursum Sani a Janbulo dake jahar Kano.

A gobe ne za a gabatar da wanda ake tuhumar agaban kotu, bayan da jami’an yan sanda suke ci gaba da gudanar da bincike akan wanda ake zargin.

Labarin kisan matashiyar ya tayar da hankulan jama’a musamman mazauna jahar, yayinda har yanzu wasu ke ta mamakin yadda wannan lamari ya kasance.

Wadda aka hallaka ɗin abaya sun taɓa yin soyayya da Quanrong kafin ta yi aure wanda daga baya suka rabu da mijinta.