Ina da lafiyar da zan jagoranci Najeriya – Tinubu

0
130

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce yana da koshin lafiyar da zai jagoranci Najeriya kuma ’yan kasar ba za su kunyata ba muddin suka zabe shi a 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin wani taron manema labarai da Kwamitin Hadin Kan Arewa na Northern Alliance (NAC)  ya shirya, dangane da halin da kasar ke ciki da kuma wasu lamura da suka shafi siyasa.

Tinubu wanda Hadiminsa na Kafafen Sadarwa, Mista Tunde Rahman ya wakilta, ya ce takarar Shugaban Kasa da yake yi a yanzu ba ta tsaya iya son ransa kadai ba, domin kuwa hakan ma amsa kira ne na ’yan Najeriya da dama da suka nuna bukatarsu a kan hakan.

“’Yan Najeriya da dama sun yi ta kirayen-kirayen da ya [Tinubu] tsaya takara kuma ba zai iya watsi da bukatarsu ba.

“Yana da koshin lafiyar da zai jogoranci kasar nan kuma babu wanda zai kunyata muddin ya samu wannan dama,” inji shi.

Haka kuma, Daraktan Yada Labarai da Hulda dda Al’umma na Kwamitin NAC, Ibrahim Madugu, ya bayyana cewa, zabar Tinubu a matsayin Shugaban Kasa, zai kasance mafificin alheri ga ’yan Najeriya da kuma kasa baki daya.

Ya bayyana cewa, “idan aka waiwaya baya, duk wani kwazo da nasarorin da Tinubu ya samu musamman a lokacin da yake gwamnati, ya yi ne don ganin Najeriya ta shawo kalubalen da take fuskanta.”

A Talatar nan ce Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar da za su fafata a Babban Zaben na 2023.

‘Yan takarar shugaban kasa da aka fitar da jerin sunayen nasu sun hada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na Jam’iyyar LP, Rabi’u Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP da Adebayo Adewole na Jam’iyyar SDP da sauransu.

 

(AMINIYA)