Buhari zai sake ciyo bashin N402bn domin biyan bashi

0
80

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na neman amincewar Majalisar Dattawa domin ciyo bashin Naira biliyan 402 da zai yi amfani da su wajen biyan bashi.

Buhari ya bayyana haka ne a wasikar da ya aike wa Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan a ranar Talata.

Ya bayyana cewa za a karbo bashin ne ta hanyar bayar da takardun lamuni domin samun kudaden da za a biya bashin Naira biliyan 375 da masu fitar daga kaya daga Najeriya suke bin Gwamnatin Tarayya.

Za kuma a yi amfani da kudaden wajen biyan jihohin Yobe Kebbi da Taraba kudadensu da suka kashe wajen gyaran titunan Gwamnatin Tarayya.

Daga cikin takardun lamunin Buhari ke sa ran samun kudin da zai biya Gwamnatin Jihar Yobe biliyan N18.623 da ta kashe kan gyaran tituna biyar na Gwamnatin Tarayya a Jihar

Ofishin Kula da Basuka na Kasa (DMO) ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kebbi ta kashe biliyan N6.706 a yayin da Gwamnatin Taraba ta kashe biliyan 2.706 wajen gyaran titunan Gwamnatin Tarayya.

Batun neman bashin na zuwa ne a ranar da DMO ta bayyana cewa yawan basukan da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 42.

DMO ya bayyana cewa an samu wannan karin ne bayan kasar ta ciyo bashin Naira biliyan 300 a cikin wata uku (Maris zuwa Yuni 2022).

A halin yanzu basukan da ake bin Najeriya sun ninka kasafin kudinta na 2023 sau biyu.

Idan aka raba wa ’yan kasar mutum miliyan 200 bashin, kowannensu zai biya Naira 210,000.

 

(AMINIYA)