Ba Buhari ne matsalar Najeriya ba – Fasto Williams

0
97

Wani limamin Kirista mazaunin Birnin London, Apostle Alfred Williams ya ce bai dace ‘yan Najeriya su dinga zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan matsalolin da suka addabi kasar ba.

Williams ya bayyana cewar yadda tsarin Najeriyar take ne ya hana shugaban aiwatar da kyawawan manufofin ci gaban da yake da shi.

Limamin yace lalacewar da aka samu a kasar ba zata bari duk wani shugaba mai zuwa samun galabar gudanar da shugabanci mai inganci ba.

Williams yace ba Buhari ne matsalar Najeriya ba, domin kuwa tsarin kasar ne mara inganci yadda koda shi ne ko Fasto Adebayo na Mujami’ar Redeem ko Fasto Kumuyi suka shiga fadar shugaban kasa, sai sun gamu da irin matsalolin da shugaban ya gani.

Limamin yace matsalar Najeriya ba daga wanda yake jagorancin kasar bane, sai dai yadda harkokin gudanar da mulki suke, wadanda muddin ba’a gyara su ba, babu wani shugaban da zai samu nasara.

Williams yace Najeriya na bukatar jagorancin da zai haifar da ci gaba a daidai lokacin da ake tunkarar zabe, yayin da ya bayyana fatan ganin kasar tayi amfani da arzikin da take da shi wajen daga darajar ta.