Dauda Dare ya sake lashe zaben dan takarar Gwamnan PDP a Zamfara

0
71

Jam’iyyar PDP ta sake ayyana Alhaji Dauda Lawal Dare a matsayin dan takararta na Gwamnan Jihar Zamfara.

AMINIYA ta ruwaito cewa, wakilai 431 daga gundumomin 147 na Kananan Hukumomi 14 da ke fadin jihar ne suka kada kuri’a a zaben fidda gwanin da aka maimaita a Gusau, babban birnin jihar.

Bayanai sun ce an dai jibge jami’an tsaro masu tarin yawa a Babbar Shelkwatar jam’iyyar, inda aka gudanar da zaben.

Shugaban Kwamitin Zaben, Sanata Hassan Felix Hayap ne ya ayyana Alhaji Dauda Lawal Dare a matsayin zakara.

Ya sanar cewa, Alhaji Dare ya samu kuri’u 422, lamarin da ya ba shi nasara a kan abokan adawarsa – Alhaji Ibrahim Shehu Gusau da Hafiz Nahuche – wadanda kowannensu ya samu kuri’a guda-guda.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Juma’ar makon jiya ce wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gusau, ta bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaben fidda gwanin takarar Gwamnan Jihar na jami’yyar PDP.

Wannan dai na zuwa ne yayin da kotun ta yi watsi da sakamakon zaben da aka gudanar tun a watan Mayu wanda Alhaji Dauda Lawal din ya zama zakara.

Bayanai sun bayyana cewa, daya daga cikin manema takarar kuma tsohon dan Majalisar Tarayya, Alhaji Ibrahim Shehu ne ya kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotun.

Da yake yanke hukuncin a makon na jiya, Mai Shari’a Aminu Baffa Aliyu, ya ce korafe-korafen da mai karar ya shigar a cikin takaradun bayanai mai shafi 109 na da madogara da hujjoji.

Mai Shari’a Aminu ya ce gudanar da sabon zabe ne zai tabbatar da adalci a tsakanin duk bangarorin da shari’ar ta shafa.