Mata sun fi maza cin jarabawar WAEC a Katsina – Kwamishina

0
116

Kwamishinan Ilimi na Jihar Katsina, Farfesa Badamasi Lawal, ya ce dalibai mata sun yi zarra kan takwarorinsu maza a jarrabawar kammala sakandare da aka rubuta a jihar a bara.

Farfesa Lawal ya bayyana haka ne a wajen bikin rufe shirin bai wa ’ya’ya mata ilimi (GEP-III) da aka gudanar a jihar ranar Alhamis.

Ya ce an cim ma wannan nasarar ne sakamakon muhimmancin da gwamnatin jihar ta bai wa ilimin ’ya’ya mata ta hanyar samar da shirye-shiryen ilimantar da su.

A cewar jami’in, dalibai 18,321 ne suka rubuta jarrabawar WASSCE a fadin jihar a bara wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyin biya.

Ya kara da cewa, “Daga cikin adadin daliban da suka rubuta jarrabawar, maza 10,441 ne, sannan mata 7,880.

“Sakamakon jarrabawar ya nuna 4,627 daga cikin dalibai mata sun samu makin ‘credit’ a darasin harshen Turanci, wato kwatankwacin kashi 58.7 cikin 100 ke nan.

“Yayin da a cikin dalibai maza su 10,441, mutum 5,632 ne suka samu makin ‘credit’ a darasin harshen Turanci, wanda ya yi daidai da kashi 54 cikin 100.

“Hakan ke nuna matan sun fi mazan kokari a darasin harshen Turanci.

“A bangaren darasin Lissafi ma matan sun fi mazan kokari, domin kuwa mata 5,678 ne suka samu makin ‘credit’, inda ake da maza 4,726 da suka samu kwatankwacin makin,” in ji Kwamishinan.

 

(AMINIYA)