An kama Farfesa da ta ci zarafin ƴar sanda a Abuja

0
62

Sifeta-Janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya yi tir da cin zarafin wata ‘yar sanda da uwargidanta ta yi.

An zargi Farfesa Zainab Duke Abiola da cin zarafin sifeta Teju Moses, saboda ta ki amincewa ta yi mata ayyukan da ba su shafi wadanda aka dauke ta aiki ta yi ba daga hukumar ‘yan sanda.

Teju na aiki ne da Farfesa Zainab, wadda ma’aikaciyar shari’a ce kuma mai rajin kare hakkin dan adam a Najeriya, a matsayin odali.

Kuma lamarin ya faru ne a gidan Farfesar da ke anguwar Garki da ke Abuja ranar 20 ga watan Satumba.

Yanzu haka Farfesa Zainab da wasu yaran gidanta da ake zargi da hannu a cin zarafin na hannun rundunar ‘yan sanda inda ake ci gaba da bincike.

Kazalika IGP Usman Alkali ya umurci a janye duka yan sandan da ke aiki da Farfesar.

Ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda matar da ke ikirarin kare hakkin bil adama za ta ci zarafin wani mutum, musamman wadda aka nada don ta ba ta kariya.

Kwanan nan ne rundunar yan sandan Najeriyar ta ba da sanarwar daukar matakin doka, ga duk wanda ya ci zarafin dan sanda ta ko wace siga.

 

(DAILYNIGERIA)