Rasha ta kare yakin da take yi a Ukraine yayin da take shan caccaka

0
113

Shugabannin kasashen duniya da suka hallara a babban zauren majalisar dinkin duniya sun ce dole Rasha ta yi bayani  kan laifukan take hakkin bil adama a Ukraine, a yayin da ministan harkokin wajen Rashar ya kare matakin kasarsa a yakin da aka shafe watanni 7 ana gwabzawa.

Batun Ukraine ne ya mamaye wannan taro na majalisar dinkin duniya, wanda a karon farko shugabannin kasashe ke yin tozali da juna tun bayan bullar annobar Covid-19.

Da yake gabatar da jawabi a taron kwamitin tsaro na majalisar a kan ta’asar da ake zargin an aikata a Ukraine tun da Rasha ta fara mamaya a ranar 24 ga watan Fabrairu, ministan harkokin wajen Rasha  Sergie Lavrov ya zargi Ukraine da laifin haifar da barazana ga tsaron kasarsa, tare da take hakkin masu magana da harshen Rashanci a Ukaraine.

Lavrov, wanda sai a lokacin gabatar da jawabinsa ya zauna a farfajiyar kwamitin tsaron, ya ce ba za su yarda da zargin da ake musu ba, inda ya ce sintirin soji na musamman da kasarsa ke yi a Ukraine ya zama wajibi ne.

An gudanar da taron musamman na kwamitin tsaron ne kwana guda bayan da shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da daukar karin dubban sojoji da za su fafata a yakin da tuni ya lakume dubban rayuka, ya daidaita miliyoyin mutane, ya lalata birane tare da illata tattalin arzikin duniya.

 

RFI