Tinubu zai chanja Najeriya cikin kankanin lokaci – Ganduje 

0
95

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje da wasu manyan yan Najeriya sun ce gwamnatin Tinubu a 2023 zai gaggauta kawo cigaba da bunkasa a kasar.

Ganduje ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amincewa da nadin da aka masa matsayin majibinci na kungiyar APC na hadin kan kasa (ANIM) a gidan gwamnatin Kano.

Ganduje yakara da cewa: “Ayyukan da Asiwaju Tinubu ya yi a baya sun nuna cewa zai iya habaka Najeriya zuwa mataki na gaba, idan an zabe shi shugaban kasa.

“Asiwaju mutum ne mai gaskiya kuma haja ne mai kyau. Ya bada gudunmawa sosai wurin habaka da cigaban demokradiyyar mu.

“Asiwaju ƙwararren ɗan siyasa ne kuma jagoran masu son kawo cigaba da suka kawo demokradiyya da muke mora a Najeriya yanzu.