Tura Mata karatu zuwa Saudiyya na da muhimmanci – Sarkin Musulmi

0
62

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a rika tura dalibai mata Jami’ar Musulunci ta Madina, domin su karanci fannin likitanci da wasu fannoni da mata ke da karanci a bangaren.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a wajen taron da Kungiyar Tsofaffin Daliban Jami’ar Musulunci ta Madina da suka shirya domin samar da guraben karatu ga dalibai masu hazaka a jami’ar.

Ya ce mata ne ginshikin ci gaban kowace al’umma, don haka bai dace a yi wasa da gudunmawarsu ba.Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya wakilci Sarkin Musulmin a taron da aka gudanar a dakin taro na Makarantar Haddar Alkur’ani ta Sarkin Musulmi Muhammad Maccido da ke Sakkwato.

Sarkin Musulmin ya ce akwai Jami’ar Musulunci ta mata zalla a Saudiyya, don haka ya kamata a karfafa wa mata gwiwa su je can domin karanta fannin kiwon lafiya, ganin yadda ake da karancin mata a wannan fanni a jihar da Arewa.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya jinjina wa tsofaffin daliban jami’ar ta Madina da ta shirya wannan taro, domin samar da guraben karatu a jami’ar.

Gwamna Tambuwal, wanda Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Bello Gwiwa ya wakilta, ya ce gwamnati ta shirya kammala tsarin doka don sauya Hukumar Bayar da Ilimin Larabci da Addinin Musulunci zuwa mataki na gaba, inda kai-tsaye za ta rika karbar umarni daga Gwamna ba wurin kwamishina ba.

Malam Mushaffa’u Musa, Sakataren Kungiyar ya ce kalubalen da aka samu a wurin taron bai fi rashin muhalli ba.

“Muna bukatar muhalli na dindindin, mutum 116 ne suka shiga karatun, maza 85 mata 31,” inji shi.

Ya yaba wa gwamnati da ta ba su dama suka yi wannan Daurar da aka samu mutane daga kananan hukumomin Sakkwato 23 da wasu jihohi, a cikin mutanen da suka ji sanarwarsu kuma suke da sha’awar shiga Jami’ar Musulunci ta Madina.

Sakataren ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Sakkwato ta samar da hanyoyi da mata za su rika tafiya kasar Saudiyya domin karatu a can, wanda hakan yana da alfanu ga ci gaban karatun mata a jihar.

Kokarin da kungiyar ta yi na samar wa mutane gurbin karatu a jami’ar, wanda shi ne karon farko da aka yi haka a Jihar Sakkwato, ya sa mutane da dama sun yaba tare da fatar a kara samun wasu su yi koyi da hobbasar da kungiyar tsofaffin daliban a nan gaba.