Yan bindiga sun budewa motocin tawagar  Sanata Uba Sani wuta a Kaduna 

0
55

bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a babban titin Kaduna-Kachia a jihar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa harin ya auku ne a Tashar Icce, kusa da garin Kujama dake karamar hukumar Kajuru.

Tawagar jiga-jigan na hanyarsu ta komawa gida ne bayan ganawa da jagororin Kiristoci a kudancin Kaduna ranar Alhamis.

A cewar Daily Trust, daya daga cikin yan siyasan da ya tsallake rijiya da baya yace kimanin motoci biyar yan bindigan suka budewa wuta.

Ya ce an yi awon gaba da mutum biyu yayinda wasu mutum uku suka jikkata. An tattaro cewa dan takaran gwamnan jihar Sanata Uba Sani, bai cikin motar saboda ya tafi Abuja daga Kafanchan.

Diraktan Kamfensa, Sani Maina, Ahmed Mayaki, da wasu jigogin jam’iyyar sun tsira.

Daga cikin wadanda aka sace sune dan takaran kujeran majalisar jiha na Kajuru, Mr Madaki, da kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Kajuru, Ruben Waziri.