‘Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 134 a Jigawa’

0
84

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ambaliyar ruwan da ake fama da ita a bana ta yi sanadin rasa rayukan mutum 134 da dukiyar da ta haura Naira tiriliyan daya da rabi a jihar.

Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Umar Namadi ne ya bayyana hakan ranar Asabar, lokacin da ya karbi bakuncin jami’in ofishin Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da ke Kano, Rihub Mahmud Farra a Dutse.

Ya ce ambiyar ta lalata tituna 22 da gadoji 11, yayin da ta tashi wani kauye baki daya.

Umar Namadi, wanda kuma shi ne mai rikon mukamin Gwamnan jihar ya ce yanzu haka ambaliyar ta tunkari Gabashin jihar kuma kananan hukumomin Kirikasamma da Birniwa na cikin barazana.

Ya ce ambaliyar ta kuma shafi mutum 272,189, wadanda daga cikinsu 76,887 suka rasa muhallansu, 134 kuma suka rasu.

Ya ce iftila’in dai ya yi sanadin raba mazauna yankunan da sauran sassan jihar.

Ya koka kan yadda ya ce madatsun ruwan jihar sun cika da yashi kuma suna bukatar a yashe su, kuma ya ce hakan ne ma ummul’aba’isun ambaliyar.

Daga nan sai Mataimakin Gwamnan ya roki Gwamnatin Tarayya da sauran kungiyoyin tallafi, ciki har da UNICEF din da su tallafa wa jihar.

Da yake mayar da jawabi, jami’in na UNICEF ya ce sun je jihar ne don kiyasta irin barnar da ambaliyar ta yi don sanin irin taimakon da za su yi mata.

Ya kuma jaddada bukatar ganin gwamnatin jihar da asusun sun yi aiki kafada da kafada don dakile aukuwar ambaliyar a nan gaba, wacce ya ce ta tasam ma zama ta shekara-shekara.