NDLEA ta kama kwalaben Akuskura da lalata gonakin wiwi a wasu jihohin Najeriya

0
81

Hukumar dake yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi wato NDLEA ta ce ta kama wani mutum mai shekara 75 da wasu mutum 21 da miyagun ƙwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce sun samu nasarar ƙwato kwalabe da capso sama da miliyan ɗaya na Akuskura da ƙwayar tramadol da kuma kilomgram 2,536 na wiwi.

Haka kuma hukumar ta ce ta lalata kadada 10 ta gonar wiwi a Jihohin Edo da Adamawa.

Hukumar ta ce a Jihar Kwara kawai, kwalabe 19,878 na Akuskura suka kama a kan hanyar Illorin zuwa Jebba.

BBCHAUSA