HomeLabaraiISWAP ta sace 'dan sanda da wasu mutum 7 a Borno

ISWAP ta sace ‘dan sanda da wasu mutum 7 a Borno

Date:

Related stories

Abba gida-gida ya lashe zaben gwamnan Kano

Hukumar Zabe ta Kasa, INEC ta sanar da cewa...

INEC na neman ta ce zaben gwamnan Kano ‘Inconclusive’ ne — Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, sanata Rabiu...

Zaben gwamnan Kano: Ratar kuri’ar da ke tsakanin NNPP da APC

Bayan bayyana sakamakon kananan hukumomi 44 na zaben gwamnan...

Jami’in tattara sakamakon zabe ya yanke jiki ya fadi a hedikwatar INEC a Kano

Jami’in tattara sakamakon zabe, Farfesa Muhammad Yushau na karamar...

Sakamakon zaben gwamnonin jihohin Najeriya

Wannan shafin zai rika kawo muku kammalallen sakamakon zaben...

’Yan ta’addan kungiyar ISWAP sun kai wani harin ba–zata a jihar Borno, inda suka yi awon gaba da dan sanda da kuma ’yan sa–kai na rundunar CJTF guda hudu da mafarauta guda uku.

Maharan sun kai farmakin ne da sanyin safiyar Asabar a karamar hukumar Gubio da ke jihar ta Borno.

Bayanai na nuni da cewa an yi awon gaba da jami’an tsaron ne bayan da ’yan ta’addan suka mamaye inda suke da zama.

Majiyar ’yan sanda ta shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi cewa an kai wa jami’an tsaron hari ne a wata RUGA da ke kauyen Pompom Baliya da ke da tazarar kilomita biyar daga garin Gubio.

’Yan ta’addan sun kuma dauke motar sintiri kirar Hilux guda daya da makamai sannan suka nufi kauyen Gadai da ke karamar hukumar Nganzai.

 

AMINIYA

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories