‘Yan bindiga sun budewa wani dan kasuwa wuta a Kano

0
49

Hukumomi a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya sun tabbatar da wani hari da ake zargin wasu ƴan bindiga sun kai a kasuwar Sabon Gari wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wani.

Shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Ibrahim Abdullahi Muhammad ne ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin inda ya ce harin ya shafi wani mai sayar da batir a kasuwar wanda ƴan bindigar suka buɗe masa wuta lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa, sai kuma wanda ya jikkata sakamakon harbi a ƙirji da cinya da hannu kuma a cewarsa, yana samun kulawa a wani asibiti da ke jihar.

A cewarsa zai yi wuya a iya tantance yawan mutanen da lamarin ya shafa saboda a lokacin da aka kai harin, mutane suna ta neman tsira “wani ma tun da bindiga ce ya ji harbi, ko da ya faɗi ya ji ciwo zai iya tashi ya gudu.”

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce zuwa yanzu hankalin jama’ar yankin ya kwanta saboda gwamnati ta jibge jami’an tsaro domin sa ido.

Ya ce duk da babu cikakken bayani game da harin, rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun je ne a kan babura.