‘Yan sanda sun kama motoci makare da makamai da za’a kai Katsina

0
71

Rundunar ’Yan Sanda a jihar Legas ta kama wasu motocin bas guda biyu da aka gano albarusai da babura guda uku da wasu kunshin kaya a cikinsu.

Kakakin rundunar a jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai ranar Asabar a Legas.

Ya ce sun kama mutanen ne masu shekara 35 da 36 da kuma 50, da ke kan hanyar tafiya Katsina, a sashen Poromope a kan hanyar Ijede da ke Ikorodu.

Kakakin ’yan Sandan ya bayar da lambar Motocin biyu da aka kama kamar haka: KMC 438 YK da kuma KMC 394 XF.

Benjamin ya ce duka motocin da babura da albarusai masu rai da sauran kunshin kayan an tura su zuwa hedkwatar ’yan Sanda da ke Ikeja a Legas domin ci gaba da bincike.

 

AMINIYA