Gwamnatin Tarayya ta fara cigiyar ‘yan kasuwar da za su zuba jari don ta jinginar musu da titunan jirgin kasa na Legas zuwa Ibadan da na Abuja zuwa Kaduna da kuma na Itakpe-Warri.
Ministan Sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar kan samar da kudaden tafiyar da harkokin sufurin Najeriya, a taron hadin gwiwar tattalin arziki na kasa da kasa da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka.
“Sauran damarmakin sun hada da garanbawul ga sabon layin dogo da aka gina na Abuja zuwa Kaduna (mai nisan kilomita 187.5) da na Warri zuwa Itakpe-Ajaokuta (mai nisan kilomita 326) da kuma na Legas zuwa Ibadan (mai tsawon kilomita 118),” inji shi.
Sambo ya kuma yi tsokaci game da muhimmancin bunkasa sufurin jiragen kasa na cikin jihohi, da suka hada da na Kaduna zuwa Zaria, da Kaduna zuwa Kafanchan da kuma Kano zuwa Chalawa.
Wanda za a gudanar na jiha zuwa jiha kuma a cewarsa su ne na Kaduna zuwa Minna, sai Kano zuwa Nguru, da kuma Legas zuwa Oshogbo.
Haka kuma akwai gyare-gyaren manyan tashoshin jiragen kasa domin samar da shagunan kasuwanci na zamani da wuraren sauke kaya a tashar jirgin kasan Iddo da ta Ebute-Metta a Legas da Ilorin a Kwara da Minna a Neja da Kaduna da Kano da Fatakwal a Ribas da Aba da Umuahia a jihar Abiya.
Sauran sun hada da na Enugu da Makurdi a Binuwai da Jos a Filato da Gombe da Maiduguri a jihar Borno, wadanda ya ce su ma akwai damar zuba hannun jari.
Ministan ya kuma ce akwai wata damar saka hannun jarin a bangaren tashoshin ruwa, musamman ma na Badagry, da Legas, da Ibaka, da Akwa Ibom, da sauran tashoshin ruwa da ake sirin samarwa.