Artabun sojoji da Boko Haram ya sa an rufe hanyar Damboa

0
199

An rufe babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa bayan sojojin Rundunar Operation Hadin Kai sun yi artabu da mayakan Boko Haram.

Aminiya ta sami rahoto cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun kai harin kwanton bauna ne a kan ayarin motocin fasinja da sojojin ke rakawa daga Maiduguri zuwa Damboa a daidai kauyen Falouja a Jihar Borno.

Wata majiyar tsaro ta ce ’yan ta’addar sun far wa sojojin da makamin roka, kafin su bi su da harbin bindiga.

Wata majiya a yankin da ta tsallake rijiya da baya, ta ce harin da ya haifar da musayar wuta tsakanin ’yan ta’addan da sojoji, ya tilasta wa fasinjojin da ke cikin ayarin motocin guje-guje domin tsira da rayukansu.

Majiyoyin sun ce soja daya ya mutu bayan da ya samu raunukan harbin bindiga, yayin da wasu uku da suka jikkata aka kai su Asibitin Damboa domin yi musu magani.

“Duk da harin da ’yan ta’addan suka kai, sojojin sun yi nasarar kare dukkan fasinjojin motocin,” in ji su.