Majalisar wakilai ta dage zamanta saboda daukewar wutar lantarki

0
92

Majalisar Wakilai ta dage zamanta na ranar Talatar nan saboda daukewar wutar lantarki da ta fuskanta.

Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya wajabta tare da sanar da dage zaman yayin da hasken lantarkin ya dauke kwatsam ana tsaka da zaman majalisa.

Rahotanni sun bayyyana cewa, wannan dai shi ya tilasta wa ’yan majalisar fita cikin duhu babu shiri, inda suka rika amfani da filitun wayoyinsu na salula suna haska hanya.

Lamarin dai na faruwa na bayan kwana guda da daukewar wutar lantarki a manyan biranen kasar ciki har da Legas da ya kasance babban birnin kasuwanci da kuma Abuja, babban birnin kasar.

Daukewar wutar lantarkin dai ita ce karo na bakwai da aka fuskanta a shekarar nan ta 2022.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki sun fitar da sanarwar ankarar da abokan huldarsu dangane da halin da ake ciki, suna mai ba da hakurin za a shawo kan matsalar nan ba da jimawa ba.

 

AMINIYA