Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 23, ta raba 116,000 da muhallansu a Benue

0
49

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Benuwe (SEMA), ta ce akalla mutane 23 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar tun bayan faduwar damina.

Sakataren zartarwa, Dakta Emmanuel Shior ne, ya sanar da hakan yayin da yake kaddamar da rabon kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a ranar Talata a Makurdi.

Ya ce mutane 116,084 ne kuma suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a wasu sassan jihar.

“Mutane 74 na fama da raunuka daban-daban. 14 daga cikin 23 da sun mutu a sakamakon hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guma,” inji shi.

Sakataren zartaswar ya kuma bayyana cewa kawo yanzu ambaliyar ta shafi gonaki hekta 14,040 yayin da gidaje 4,411 suka nutse.

“Makaranta da kasuwanni, kamfanoni, gidaje da filayen noma da ke yankuna 104 abin ya shafa,” in ji shi.

Ya lissafa kananan hukumomin da abin ya shafa kamar haka, Guma, Vandeikya, Otukpo, Katsina-ala, Makurdi, Apa, Agatu, Tarka, Gboko, Gwer-West da Logo.

“Wadanda abin ya shafa na bukatar agajin gaggawa. Wannan shi ne dalilin wannan aiki namu.

“Mun fara ne da Makurdi da Agatu saboda su ne suke da mutane 34 da 28 da abin ya shafa.

“Wadanda abin ya rutsa da su a Agatu da a halin yanzu suka fake a babbar hanyar tarayya nan ba da jimawa ba za a koma Obagaji,” in ji shi.

Shima da yake jawabi a wajen taron, babban jami’in bincike da ceto na hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, John Digah, ya ce hukumar ta tura na’urar kula da ruwa domin tallafa wa wadanda abin ya shafa da ruwan sha.

Digah ya ce na’urar tana da karfin maganin lita 2,000 na ruwa a cikin sa’a guda.

“A cikin kwanaki biyun da suka gabata mun yi jinya tare da raba wa wadanda abin ya shafa ruwan lita 140,000,” in ji shi.