Yan bindiga sun kashe babban yaron dan majalisa a Bauchi

0
118

Babban ‘dan Honarabul Bala Ali, Dan majalisa mai wakiltar mazabar Dass a majalisar dokokin jihar Bauchi ya mutu a hannun yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Jaridar Punch ta ce mai magana da yawun majalisar, Abubakar Suleiman, Abdul Barra, ya bayyana hakan a takardar da ya baiwa manema labarai ranar Talata.

Yace dan majalisa mai wakilatar mazabar Burra, Ado Wakili, ya sanar da mutuwar yaron abokin aikinsu a zauren majalisa.

Yan majalisan sun aike sakonnin ta’aziyyarsu ga iyalan Honarabul Bala Ali inda sukayi addu’an Allah ya jikan mamacin.