‘Yan ta’adda sun kashe fararen hula 14 a Jamhuriyar Congo

0
84

Wasu mayakan ‘yan tawaye sun daddatsa fararen hula 14 har lahira a wani farmaki da suka kaddamar a yankin gabashin Jamhuriyar Demokaradiyar Congo a karshen makon nan.

Ana zargin mayakan ‘yan tawayen ADF da kutsawa cikin kauyen Kyamata da ke lardin Ituri, inda suka kashe fararen hula 14 ta hanyar daddatsa su da adduna.

Mayakan sun kuma raunata wasu mutanen tare cinna wa gidaje akalla 36 wuta a kauyen na Kyaamata.

Majiyar sarakunan gargajiya na wannan yankin ta tabbatar da aukuwar harin, kuma a cewarta, kashi 70 na jama’ar kauyen sun kaurace wa gidajensu.

Kungiyoyin mayaka masu dauke da bindiga sun sha far wa jama’ar yankin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, kuma akasarin mayakan sun kasance ribatattun yakin da ya barke a kasar ne a tsakan-kanin shekarun 1990 zuwa farko-farkon shekarun 2000.

Daga cikin wadannan kungiyoyin har da na mayakan ADF wanda aka ce suna da alaka da mayakan IS.

Ana zargin ADF da yanka dubban fararen hula a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo tare da kaddamar da hare-haren bama-bamai a Uganda mai makwabtaka da kasar.

RFI