HomeLabaraiAn kori manyan ’yan sanda 7, an rage wa 10 matsayi kan...

An kori manyan ’yan sanda 7, an rage wa 10 matsayi kan rashin da’a

Date:

Related stories

Hukumar DSS ta kama wasu bata gari da ke sayar da sabbin takardun kudi na Naira

Ma’aikatar harkokin wajen kasar a ranar Litinin din nan...

Yadda lamari ya kasance yayin zuwan Buhari Kano don kaddamar da aiyuka 8

An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano da...

Najeriya ta yi asarar likitoci 2800 a cikin shekaru biyu – NARD

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NARD, Dr Innocent Orji ya...

Yadda ake canzar da kudin Sepa zuwa Naira a yau Litinin

Farashin Separ Nijar zuwa Naira a farashin kasuwar canjin...

Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda (PSC) ta kori mayan jami’an ’yan sanda bakwai daga aiki tare da rage wa wasu 1o matsayi saboda aikaa ba daidai ba.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne yayin ci gaba da babban taronta karo na 15 wanda ake sa ran kammalawa ya zuwa ranar Alhamis.

Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ta shaida wa ’yan jarida wadanda lamarin ya shafa sun hada da masu mukamin CSP daya da SP daya da kuma ASP biyar.

Wadanda aka rage wa matsayi sun hada da mutum daya daga CSP zuwa SP, uku daga SP zuwa DSP, biu daga DSP zuwa ASP, hudu daga ASP zuwa Sufeto da dai sauransu.

Taron, wanda ke gudana karkashin jagorancin mukaddashin shugaban hukumar, Mai Shari’a Clara Ogunbiyi, an gabatar masa da korafi kan laifuffuka 47 da ake zargin ’yan sanda sun aikata, domin daukar matakin da ya dace.

Haka nan, taron ya saurari daukaka karar da wasu ’yan sanda da aka kora daga aiki suka yi.

Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ta shaida wa ’yan jarida wadanda lamarin ya shafa sun hada da masu mukamin CSP daya da SP daya da kuma ASP biyar.

Wadanda aka rage wa matsayi sun hada da mutum daya daga CSP zuwa SP, uku daga SP zuwa DSP, biu daga DSP zuwa ASP, hudu daga ASP zuwa Sufeto da dai sauransu.

Hukumar ta ja hankalin ’yan sanda da su rika gudanar da ayyukansu daidai da doka, tana mai cewa za ta nuna halin ba-sani-ba-sabo wajen daukar matakin kan duk wanda aka kama da take doka.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories