Nnamdi Kanu ya rubutawa gwamnati wasika da ta sakeshi cikin gaggawa

0
86

Jagoran kungiyar ‘yan a-ware ta IPOB da ke tsare, Nnamdi Kanu, ya aika takardar korafi ga shugaba Muhammadu Buhari inda ya nemi gwamnati ta sake shi cikin gaggawa.

Gwamnatin Najeriya na tuhumarsa da laifuka guda 11, ciki har da cin amanar ƙasa da ta’addanci, da mallakar haramtattun makamai, da kuma kokarin tunzura jama’a don haifar da yamutsi.

A cikin wasikar wadda rukunin lauyoyinsa karkashin jagorancin Mike Ozekhome mai lambar SAN suka fitar, Nnamdi Kanu ya bukaci Shugaba Buhari ya ba da umarnin sakin sa daga hannun hukumar tsaron farin kaya ta DSS don bin wata hanyar cimma masalahar siyasa.

Wasikar ta ce: “Kana iya yin hakan ta hanyar umartar ministan shari’a na tarayya don ya yi amfani da ikonsa a karkashin sashe na 174 na tsarin mulkin 1999 ya shigar da kudurin ‘babu muradin gurfanarwa a kotu wato (nolle prosequi)’.

“Hakan zai kawo karshen zaman dar-dar din da ake fama da shi da kuma umarnin zaman gida da a yanzu suka addabi yankin Kudu maso Gabas kuma ya kassara harkokin kasuwanci da rayuwa kamar yadda aka saba”, in ji takardar ta Nnamdi Kanu kamar yadda jaridar vanguard ta ruwaito.