Malamai sun bijire wa ASUU sun dawo aiki a jami’ar Nassarawa

0
104

Wasu malaman Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, NSUK, sun bijire wa umarnin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, inda su ka dawo bakin aiki duk da ganin aikin da a ke yi.

Dakta Samuel Alu, shugaban kungiyar ASUU, reshen NSUK, Abraham Ekpo, jami’in yada labarai da tsare -tsare na cibiyar da Najeem Gbefwi, shugaban kungiyar daliban NSUK, SUG, ne su ka tabbatar wa manema labarai wannan ci gaban a cibiyar da ke Ƙaramar Hukumar Keffi a yau Alhamis. .

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, wanda ya bi diddigin lamarin, shi ma ya zagaya ɗakunan karatun ya kuma tabbatar da cewa ana gudanar da laccoci a tsangayar shari’a, da bangaren ilimin zamantake wa da dai sauransu.

Kamfanin dillancin labaran ya rawaito cewa komawa aikin na malaman ya zo ne biyo bayan sanarwar da jami’ar ta yi na cewa ɗalibai su koma makaranta, amma sai ASUU reshen NSUK ɗin ta soki matakin.

Kungiyar kwadagon a cibiyar ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin da hukumar ta kasa ke ci gaba da yi har sai gwamnatin tarayya da kungiyar ta kasa su cimma matsaya kan bukatun ta.

Da yake magana game da wannan ci gaban, Ekpo ya bayyana hakan a matsayin nasara ga kowa da kowa..

“Bayanan da muke da su na cewa an fara laccoci a ko’ina amma kun san wannan abu ne sai a hankali. Mu na da sassan da suka fitar da jadawalin su jiya.

“Don haka abu ne da ke faruwa cewa duk makon farko na koma wa makaranta ba a samun cikowar ɗalibai. Na tabbata nan da mako mai zuwa, za ku ga jama’a masu yawa, kuma ayyukan karatu za su zama na yau da kullum,” inji shi.