Gwamnatin tarayya ta ayyana 10 ga Oktoba a matsayin ranar hutun Maulidi

0
55

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 10 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan Mauludi na tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Sakataren dindindin na ma’aikatar harkokin cikin gida, Shuaib Belgore, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a jiya Alhamis a Abuja.

A cewarsa, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya ɗaukacin al’ummar musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar zagayowar watan Maulidi.

Ministan ya hori daukacin ƴan Najeriya da su kasance cikin ruhin soyayya, hakuri da juriya da sauran kyawawan ɗabi’u, wadanda Manzon Allah ya buga misali da su.

Ya ce yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.