Mutane biyu sun mutu a wani hatsarin mota a jihar Jigawa

0
90

Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Kiyawa zuwa Jahun a jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

A cewar Shehu Adamu, lamarin ya shafi wata motar bas Toyota mai launin toka mai lamba MGM435XA, inda take jigilar fasinjoji zuwa Maiduguri da ke jihar Borno.

Ya kara da cewa hatsarin ya afku ne a hanyar Kiyawa zuwa Jahun, inda fasinjoji biyu suka mutu namiji da mace.

“A ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoba, 2022, da misalin karfe 06:00 na safe, hatsarin ya afku a kusa da kauyen Katika lokacin da direban motar ya rasa iko da motar sakamakon tukin wuce sa,a, inda ta yi karo da wata bishiya a bakin hanya,” acewar Shehu adamu.

Kakakin Hukumar NSCDC ya ce, nan take aka kwashe wadanda hadarin ya rutsa da su, aka garzaya da su cibiyar kula da lafiya a matakin farko da ke karamar hukumar Kiyawa.

“an tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu da suka samu raunuka dabadan daban harda da direban bas din, kuma an tura su zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya dake Azare, a Jihar Bauchi,

Ya bayyana sunayen marigayin da Muhammad Atiku, mai shekaru 27; da Cecilia Peter,mai shekaru 21.

Shehu ya kara da cewa, “rundunar ta bukaci jama’a da su rika tuka mota acikin nutsuwa a kodayaushe, su guji wuce gona da iri da kuma tukin wuce sa’a a kan titi.