Buhari ya bai wa mawakiya Teni lambar girmamawa ta kasa

0
134

Fitacciyar mawakiyar Najeriya, Teniola Apata, wacce aka fi sani da Teni, ta samu lambar girmamawa daga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A ranar Talata ne mawakiyar ta wallafa bidiyon karramawar ta shafinta na Instagram, inda ta ce shugaban ya damka mata lambar girmamawa ta OON.

Teni dai na daga cikin jerin ’yan Najeriya da aka gudanar da bikin karrama su a ranar Talata a Abuja.

Matashiyar mawakiyar wadda ’yar uwarta, Niniola ta jima da yin fice kafin ta, ta fara shahara ne da wakarta ta Fargin.