Gwamnati za ta karrama mashahurin malamin musulunci, Sani Rijiyar Lemu

0
79

Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu yana cikin muhimman mutanen da gwamnatin tarayya za ta ba lambar karramawa na shekarar 2022. Legit.ng Hausa ta fahimci gwamnatin Muhammadu Buhari za ta bada lambar girman OON ga babban malami, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu.

A wata takarda da ta fito daga ofishin Ministan harkoki na musamman, an ji cewa an gayyaci shehin a cikin mutanen da za a karrama a shekarar bana. Kamar yadda takardar da Mai girma Minista watau Sanata George Akume ya aikawa malamin ta nuna, za ayi wannan biki yau a dakin taro na ICC a Abuja.

Ana sa rai yanzu haka Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu yana garin Abuja inda za ayi bikin.