Gwamnatin Najeriya ta shiga tsakanin rikicin Dangote da jihar Kogi

0
122

Fadar gwamnatin Najeriya ta shiga tsakanin rikicin da ya kunno kai tsakanin gwamnatin jihar Kogi da hamshakin Attajirin Afirka Aliko Dongote, dangane da mallakar katafaren kamfaninsa na siminti da ke Obajana.

Bayanai sun ce an gana tsakanin shugaban rukunonin kamfanin na Dongote da kuma gwamnan jihar Kogi Yahya Bello da kuma takwaransa na jihar Nasarawa Abdullahi Sule.

Yukurin sulhun da fadar shugaban Najeriya ta yi, ya zo ne, bayan matakin da gwamnatin Kogi ta dauka na rufe katafaren kamfanin simintin Obajana, bisa zargin kauracewa biyan haraji, da kuma rashin fayyace gaskiyar hakkin mallakar kamfanin.

Wasu majiyoyi sun ruwaito cewar shugabannin rukunin kamfanonin na Dangote sun kammala shirin tunkarar kotu a wannan makon kan al’amarin, ciki kuwa har da yadda  ‘yan banga na gwamnatin

Kogi suka kai farmaki kan katafariyar masana’antar simintin da ke Obajana, inda ake zargin sun jikkata ma’aikata da dama tare da rufe kamfanin.

A ranar Alhamis da ta gabata, gwamnatin jihar Kogi, ta gabatar da rahoton kwamitin kwararru na musamman kan tantance halaccin mallakar kamfanin simintin na Obajana.

Yayin gabatar da rahoton, sakatariyar gwamnatin jihar ta Kogi Mrs Folashade Ayoade ta ce ba a bi ka’ida ba wajen mika Obajana zuwa kamfanin Dangote.

haka zalika  wasu takardun shaida guda uku da suka tabbatar da cewa gwamnatin Kogi ce ta mallaki kamfanin simintin na Obajana , an yi amfani da su wajen karbar bashin naira biliyan 63 da Dangote ya yi.