Wasu yan bindiga sun kone hedikwatar karamar hukuma a ebonyi

0
106

Rundunar ‘yansandan Jihar Ebonyi ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wani sashe na hedikwatar karamar hukumar Ezza ta arewa.

A cewar NAN, ‘yan bindigar sun kuma kone kadarorin a yayin harin da suka kai a safiyar ranar Litinin, Chris Anyanwu, kakakin rundunar ‘yansandan Ebonyi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin.

“Muna sane da harin amma har yanzu ba mu samu cikakken bayani ba. A yanzu haka ana ci gaba da bincike domin samun cikakken bayani amma ba a kama su ba,” inji shi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wani taron manema labarai, shugaban karamar hukumar Ogodo Nomeh, ya ce da yawa daga cikin ‘yan bindigar sun samu raunuka yayin da suke artabu da jami’an tsaro.

“‘Yan ta’addan sun yi artabu da jami’an tsaro a cikin karamar hukumar a wani artabu da bindiga,” in ji shi.

“Wasu daga cikin ‘yan bindigar sun samu raunuka da harbin bindiga. Kawo yanzu dai ba a kama kowa ba saboda lamarin ya faru ne cikin dare.

“An yi harbe-harbe da yawa kuma da yawa daga cikin ‘yan bindigar sun jikkata.

“A yanzu haka, muna tafiya daga wannan asibiti zuwa wancan don duba mutanen da suka samu raunukan harbin bindiga.

“Ba mu zargin kowa a yanzu ba har sai mun kama wadanda ake zargin. Kun san abin ya faru ne da misalin karfe biyu na dare.

“Muna tattaunawa da jami’an tsaro da suka yi artabu da ‘yan ta’addan.”