‘Yan bindiga sun yi barazanar aure ‘ya’yan tsohon akanta-janar na zamfara

0
111

‘Yan bindiga sun fitar da wani faifan bidiyo na ‘ya’yan tsohon Akanta-Janar na Jihar Zamfara, Abubakar Bello Furfuri da suka sace.

Harin da suka kai gidan tsohon Akanta -Janar na jihar ya faru ne watanni hudu da suka gabata.

A cikin faifan bidiyon, wadanda suka yi garkuwa da su sun yi barazanar auren ‘yan matan ko kuma su tilasta musu su zama masu tayar da kayar baya.

faifan bidiyon ya nuna ‘yan mata hudu a tsaye, dauke da makamai da harsashi.

Uku daga cikinsu sun saka hijabi. Ita daya daga cikinsu kuma ta yi magana cikin harshen Hausa, inda ta dinga kuka.

Leadership Hausa ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun ki sakin wadanda suka sace duk da karbar makudan kudade daga iyalansu.

An yi garkuwa da mutanen ne a daren ranar 5 ga watan Yuni a unguwar Furfuri da ke karkashin karamar hukumar Bungudu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa an kama mutane kusan 20; wanda akalla rabin adadinsu mata ne.
Maharan sun yi gaggawar ficewa daga kauyen kafin jami’an tsaro da aka tura yankin su isa wurin.