Ba za mu sake amincewa da magudin zabe a Kano ba – Abba Gida-Gida

0
94

Dan takarar Gwamnan Jihar Kano na NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya ce jam’iyyar da magoya bayanta ba za su sake amincewa da inkonkulusib ba a zaben 2023.

Dan takarar da aka fi sani da Abba Gida-Gida ya ce a shirye suke a su gudanar da yakin neman zabensu na 2023 ba tare da yaudara ko cin zarafi ba, don gudun tayar da zaune tsaye.

Da yake ganawa da manema labarai a Kano, Abba ta bakin kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya ce, “A wannan karon, ba za mu amince da duk wani nau’in tsoratarwa daga kowane bangare ba.

“Za mu yi tsayuwar daka don ganin an bar dimokuradiyya ta yi aikinta, musamman wajen amfani da sabuwar dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima,” in ji shi.

Ya ce la’akari da yawan masu rajistar zabe a Kano da kuma yadda jama’a suke da aniyar yin fitar farin dango don yin zabe, ya sanya suke da kwarin gwiwar samun nasara.

“Madugunmu, kuma dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso kansa na cike da mamakin ci gaba da jajircewar da magoya baya da kuma al’ummar Jihar Kano ke nuna masa tun daga lokacin da ya fito takara a shekarar 2019,” in ji Abba.