ASUU ta janye yajin aiki

0
93

Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana gudanarwa a Najeriya.

Kungiyar ta yanke yanke shawarar janye yajin aikin ne a babban taron Majalisar Zartarwarta da ya gudana a Abuja.

A safiyar Juma’a wani babban jami’in ASUU da ya halarci taron ya ce, “Gaskiya ne, mun janye yajin aikin… Na gaba da safiyar nan Shugaban ASUU na Kasa zai fitar da sanarwar a hukumance.”

Wata takwas cif ke nan da malaman jami’o’in gwamnati suka yi suna yajin aikin da kungiyar ta kira tun ranar 14 ga ga watan Fabrairu, 2022.