Sayen kuri’u zai mamaye zaben 2023 – Dakta Hakeem

0
91

A ranar Alhamis 6 ga watan Oktobar 2022, shirinmu na Barka Da Hantsi Nijeriya da muke gabatarwa a Manhajar Podcast ya karbi bakuncin mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF, DAKTA HAKEEM BABA-AHMED, inda aka yi tattaunawa ta musamman game da harkokin zaben 2023.

A cikin shirin, ya bayyana wasu abubuwa da dama game da zaben 2023 tun daga kan yakin neman zabe har zuwa zaben kansa. Kana ya yi waiwaye a kan irin siyasar da aka gudanar a jamhuriyoyin baya a Nijeriya har ma da yadda suka shawo kan hatsaniyar da wakilin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a wurin tattara sakamakon zaben 2015, Mista Orubebe ya tayar yayin da ya ga dan takararsu zai sha kasa.

Ya kake kallon yadda aka fara gudanar da yakin neman zabe a bana?
Wato wannan zaben da za a yi yana da abubuwa guda uku wadanda suka bambanta da sauran hada-hadar zabe.

Na daya dai, an canza dokar zabe tare da kara tsawon lokacin yin hada-hadar zabe kamar irin su taron gangami na neman magoya baya da yawace-yawace yakin neman zabe da irin kamfe da ake yi a rediyo da talabijin wanda aka kara shi zuwa kwana 150 fiye da wata uku, wanda ya kasance dogon tsere ne.An fara shi tun daga yanzu kuma ina tsammanin za a ci gaba har ya rage mako guda ko biyu kafin fara zabe, wanda abubuwa da yawa na iya faruwa kuma zan fada wasu da ke da muhimmanci.

Na biyu, ba mu taba yin zabe wanda manyan jam’iyyu suka shiga cikin irin wannan hada-hadar yakin neman zabe da rikice-rikice a tsakaninsu ba.

A baya sukan warware wadannan rikice-rikice lokacin da aka fitar da dan takara, amma har yanzu ana nuna wa juna yatsa.

Na uku kuma, Akwai kuma damuwa na yuwuwar amfani da addini da bangaranci da kabilanci a cikin wannan zabe fiye da kowani lokaci.

Magana ta karshe kan wannan zabe da ya bambanta da sauran zabuka shi ne, yadda aka fito da wani salo na gurbata zabe, wanda za a bari a je har inda mutum yake da katin zabe a ba shi kude a ce masa ya dangwala a nan, wato wakilan jam’iyya wadanda aka dora musu amanar su nesanta musu jefa kuri’a da sauran jama’a su suke yin haka.

Ka san yadda ake yi za ka zo a tantance ka a tabbatar cewa ka cancanta ka yi zabe, sannan ka koma gefe, idan aka shirya zabe sai ku yi layi, ga wanda zai ba ku takardun jefa kuri’a, sai ka dauke ka je wurin da za ka dangwala wanda ake so sai ka saka a cikin akwatin zabe.

Yanzu kuma an fito da wani tsari na banza wanda tun ana yi kadan-kadan har ya zama ruwan dare. Inda ake ce wa mutum ga dubu daya ko biyu ko biyar ka dangwala wa wannan.

Takamaimai su waye suke yin wannan abun?
Dukkan jam’iyyu suna yi. Mutane ne wadanda aikinsu kenan.

Suna bangaren hukumar zabe ne ko kuma suna bangaren jami’an tsaro?
Ba sa ko daya, amma da yardarm jami’an hukumar zabe da kuma jami’an tsaro. Domin ba a ma yarda wani ya kusanci wanda yake zabe ba.

Kamar yadda na fada maka, za ka je wurin zabe sannan ka bi layi, idan aka zo kanka, sai ce kawo katinka a duba abubuwan da ake bukata domin a tabbatar ka cancanta katinka ne kuma akwai sunanka a rubuce, sai a ce je ka tsaya can ko je ki tsaya a can a jira.

Idan aka zo yin zabe kuma kai kadai daga kai sai Allah, sai katin jefa kuri’a, sai kuma akwatin zabe. A tsakanin wannan wurin, akwai wadanda za su zo su bayar da kudi domin dangwalawa wani, wasu ma har sai sun dauki hoton wand aka dangwalawa.

Wanda shi ake kira sayan kuri’u kuma ana amfani da shi a jihohi da yawa, da alama wannan zabe za a yi irin wannan abu.

Misali, wani zai iya cewa da wace jiha da wace jiha wannan abu ya faru?
Ya faru a zabukan da aka yi kamar na jihohin Osun da Ekiti da kuma Anambra, kuma dukka abin da jam’iyyu ke shiryawa har da wannan abu a ciki, sannan akwai kudaden da aka killace domin shi.Magana ta karshe shi ne, za a yi zabe wanda yake da matsala wata kila ma a hana wasu wurare yin zaben, saboda rashin kwanciyar hankali na rashin tsaro.
A nan arewa akwai jihohi kamar irin Kaduna, Zamfara, Sakkwato, Kebbi da Neja, wurare da yawa saboda barazanar ‘yan ta’adda wadanda suke rike da kauyuka suna iya hana zaben gaba daya.