‘Yan bindiga sun kashe mutum tara a Zamfara

0
79

‘Yan fashin daji sun yi harbin mai uwa-da-wabi kan mutanen da suka je cin kasuwa a Tashar ‘Yar Sahabi cikin yankin Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, inda suka kashe mutum tara.

Wani shaida ya ce ƙarin mutum biyar ne suka sami raunuka, cikinsu har da ƙananan yara da tsofaffi sanadin harbe-harben na ranar Alhamis.

A yankin Shinkafi ma, bayanai sun ce motoci sun kasa tashi daga garin zuwa Ƙauran Namoda kwana guda bayan an yi wa wata motar fasinja ruwan harsasai a kan hanya.

Da tsakar rana ne, ‘yan kasuwa suka ji tashin bindigogi ana tsakiyar cin kasuwa a Tashar ‘Yar Sahabi.

Cikin waɗanda aka kashe har da mata guda uku da su ma suka je cin kasuwa.

Tuni aka kai mutanen da suka jikkata zuwa asibitin Magami.

Wani shaida ya ce ga alama zuwan sojoji ne ya katse hanzarin maharan, inda suka yi musayar harbe-harbe har cikin daji.

Shaidu sun ce Tashar ‘Yar Sahabi kamar sauran yankunan Zamfara da dama hare-haren ‘yan fashin daji sun sake ƙazancewa.

A garin Dan Sadau da kewaye, mutane ba sa iya zuwa gona ba tare da an musu fashin babur, ko an ɗauki mutum har sai an biya kuɗin fansa ba.

Haka zalika, ƙauyuka da yawa a gabashin Magami, ba su iya noman kirki ba, saboda ‘yan fashi kan je a kullum su kwashi mutane kan babura su kai can gonakinsu, su yi ta nomewa.

Harin Tashar ‘Yar Sahabi na zuwa ne kwana guda bayan ‘yan fashi sun buɗe wuta kan wata motar fasinja a kan hanyar Shinkafi zuwa Ƙauran Namoda.

Wani shaida shi ma ya ce fasinjojin da aka kashe huɗu, mata ne da ke kan hanyarsu ta komawa ƙauyen Lugu cikin Ƙaramar Hukumar Issa, kafin su taras da ajalinsu ranar Laraba.

BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu amma bai amsa kiraye-kirayen aka yi masa ba.

Wasu majiyoyi a Zamfara sun ce hare-haren ‘yan fashin daji sun ta’azzara ne wannan lokaci a jihar sanadin tarewar da maharan suka daɗa yi.

Luguden wuta da jiragen yaƙin Najeriya ke yi ba-ji-ba-gani a jihohi maƙwabtan Zamfara sun fatattaki da yawansu daga can.

Haka zalika, batun sulhun da ake cewa an yi a jihar, ya yi matuƙar rage tasirin ‘yan sintiri masu kare ƙauyuka, jami’an tsaron da ke ƙasa kuma ba su wadatar ba.

Abin da ya bar dubun-dubatar mutane, suna ga Allah, suna ga ‘yan fashin daji.

BBC