Dayawan yan majalissar tarayya ba zasu koma ba

0
108

Aminiya ta rairayo jerin wasu ’yan Majalisar Tarayya 16 da ba za su koma zauren majalisar ba bayan Babban Zabe na shekarar 2023.

Kamar yadda dai masu iya magana ke cewa, wadannan ’yan majalisar sun ci ‘taliyar karshe’ a kujerunsu na wakilci.

A yayin da wasu daga cikinsu ba za su koma ba saboda sun tsaya takarar neman wasu mukaman siyasa daban-daban da suke yi, wasunsu kuma ba za su samu damar komawa ba ce saboda gaza kai bantensu a yayin zaben fid-da-gwanayen takara ne kujerumnsu.

Galibi, kadan ne daga cikinsu kuma suka yi watsi da neman maimaita mukamansu a Zauren Majalisar ta Kasa.

Daga cikin ’yan majalisar da za su yi bankwana da ita dai akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Yakubu Dogara da Ike Ekweremadu da Oluremi Tinubu da kuma Smart Adeyemi.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan:

Yana daya daga cikin wadanda suka fi dadewa a zauren majalisa, kuma ya soma ne daga Majalisar Wakilai, inda aka zabe shi a shekarar 1999 ya wakilci mazabar Bade da Jakusko ta Jihar yobe.

An kuma sake zabar sa a 2003 inda ya maimaita wannan kujera.

Daga wannan kuma ya koma Majalisar Dattawa inda ya wakilci mazabar Yobe ta Arewa tun daga lokacin har zuwa yanzu.

Sai dai a yanzu ba zai sake komawa majalisar ba, idan wa’adinsa ya kare a 2023, sakamakon umarnin kotu da ta ba Bashir Machina takarar kujerar tana mai tabbatar da cewa Lawan din bai shiga takarar zaben fidda gwani.

Ike Ekweremadu (mazabar Enugu ta Yamma)

Sau uku yana zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ya kuma shiga majalisar ne a shekara 2003 yana wakiltar mazabar Enugu ta Yamma.

Tun lokacin yake wakiltar wannan mazabar har tsawon shekara 20.

Ya dai sayi fom na tsayawa tsakarar Gwamnan Jihar Enugu, amma ya janye aniyarsa ta tsayawa sa’o’i kadan kafin a yi zaben fitar da gwani.

A halin yanzu dai Ekweremadu yana tsare a Ingila bisa zargin safarar sassan jikin dan Adam.

Yakubu Dogara

Shi ne tsohon Shugaban Majalisar Wakilai daga mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi.

Ya zama Shugaban Majalisar ne daga 2015 zuwa 2019, kafin rike wannan mukami, ya shugabanci kwamitoci da yawa.

Ya zama dan majalisa ne a shekarar 2007, kuma yana zauren har yanzu.

Sai dai ya yanke shawara ba zai sake komawa ba a bisa ra’ayi na kashin kansa.

James Manager (Mazabar Delta ta Kudu)

Shekararsa 20 a zauren majalisar za ta zo karshen wannan karon. Ya rike mayan mukamai a kwamitoci daban-daban na majalisar har da na makamashi, da kuma na kula da yankin Neja Delta.

Ya tsaya takarar Gwamnan Delta a jam’iyyarsa ta PDP amma ya fadi a zaben fid-da-gwani.

Abdullahi Ibrahim Gobir (Mazabar Sakkwato ta Gabas)

Sanatan mai wakiltar Mazabar Sakkwato ta Gabas ya kuma rike mukamai na jagora a Majalisar Dattawa.

Sau uku yana zama Sanata, biyu a karkashin PDP, bayan ya sauya sheka zuwa APC ya sake komawa.

Sai dai a yanzu ba zai sake komawa majalisar ba kasancewar ya nemi takarar kujerar gwamnan Sakkwato amma ya sha kaye a hannun Ahmed Aliyu.

Ajayi Boroffice (Mazabar Ondo ta Arewa)

Shi ne Mataimakin jagora a Majalisa Dattawa kuma sau uku yana zaman sanata daga mazabar Ondo ta Arewa.

Ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyarsa ta APC, amma ya janye wa Ahmed Tinubu a zaben fitar da gwani.

Ba kamar sauran ba, Ajayi da kansa ya janye daga takarar neman komawa Majalisar Dattawa.

Aliyu Sabi Abdullahi (Mazabar Neja ta Arewa)

Shi ne Mataimakin mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, ya kuma yi kokarin samun tikitin takarar kujerarsa a zaben mai zuwa amma bai yi nasara ba.

Sakamakon shan kaye da ya yi a hannun gwamna mai ci Abubakar Sani Bello wanda ke shirin tafiya Majalisar idan ya kammala wa’adin mulkinsa.

Oluremi Tinubu (Mazabar Legas ta Tsakiya)

Ita ce matar Bola Ahmed Tinubu, shekarar ta 12 a zauren Majalisar Dattawa.

Sanatar ba ta nemi ta sake komawa majalisa ba a zabe mai zuwa ba zai rasa nasaba da takarar Shugaban Kasa da mijinta Bola Tinubu ya tsaya ba.

Oluremi ta rike mukamin Shugabar Kwamitin Sadarwa a Majalisar.

Smart Adeyemi (Mazabar Kogi ta Yamma)

Tsohon Shugaban ’Yan Jarida na Kasa ne, yana kuma wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawa, inda ya kwashe shekara 12.

Sai dai ba zai sake komawa zauren majalisar ba sakamakon shan kaye da ya yi a zaben fitar da gwani na mazabarsa.

Ya dangana hakan ne ga yadda yake sukar wasu manufofin jam’iyyarsa ta APC a zauren majalisar, wanda hakan ta sa aka kayar da shi, a cewarsa.

Leo Ogar (Delta ta Kudu)

Dan Majalisar Tarayyar na jam’iyyar PDP shi ne mai wakiltar Isoko ta Arewa da ta Kudu da ke Jihar Delta.

An kuma sake zaben sa a shekarar 2007 da 2011 da 2015 da kuma 2011.

Shi ke rike da mukamin jagoran majalisar, sannan ya taba shugabancin kwamitoci daban-daban na majalisar.

Ba zai koma zauren majalisar ba ne domin bai sake neman takarar kujerar ba.

Toby Okechukwu (Enugu)

Shi ne Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai, yana kuma wakiltar mazabar Riba/Awgu/Aninri/ ta Jihar Enugu a karkashin Jam’iyyar PDP.

Ba zai koma zauren majalisar ba, sakamakon kaye da ya sha a zaben fidda da gwani a hannun Anayo Onwuegbu.

Pat Asdu (Enugu)

Shi ne yake wakiltar mazabar Nsukka/ Igbo-Eze ta Kudu ta Jihar Enugu.

Karonsa hudu yana komawa zauren majalisar a karkashin Jam’iyyar PDP.

Sai dai wannan karon ba zai koma ba, sakamakon kaye da ya sha a hannun Bitalis Abba a zaben fid-da-gwani na jam’iyyar.

Asadu ya danganta kayen da sha ga adawar ’yan Karamar Hukumar Nsukka da ya fi sauran tsanani.

Ossai Nicholas Ossai (Delta)

Ossai yana wakiltar mazabar Ndokwa/Ukwuani ta Jihar Delta.

Dan majalisar ya rike shugabancin kwamitoci daban-daban na majalisar ciki har da kwamitin yarjejeniya da tsare-tsare da tarbar baki.

Sau uku yana lashe zabe zuwa zauren majalisar, sai dai wannan karon za a yi babu shi a zauren majalisar, sakamakon kaye da ya sha a hannun Nnamdi Ezechi yayin zaben fid-da-gwani.

Herman Hembe (Binuwai)

Hemebe shi yake wakiltar mazabar Tarayya ta Jechira a Jihar Binuwai wanda ta wunshi kanana hukumomin Konshisha da Vandeikya.

Shekararsa 12 a zauren majalisar, ya kuma yanke shawarar ba zai koma ba, sakamakon tsayawa takarar kujerar gwamna da ya yi a jihar a karkashin jam’iyyar Labour a zaben 2023.

Uzoma Nkem-Abonta (Abia)

Uzoma shi yake wakiltar Ukwa ta Gabas da ta Yamma ta Jihar Abia.

Ya kuma shiga zauren majalisar ne a shekarar 2007, a karkashin Jam’iyyar PDP.

Dan majalisar ya rike shugabancin kwamitin sauraron koke-koken jama’a.

Ba zai sake komawa zauren majalisar ba a wannan karon sakamakon shan kaye da ya yi a zaben fitar da gwani na jama’iyyarsa.

Umar Mohammed Bago (Neja)

Shi yake wakiltar mazabar Chanchaga ta Jihar Neja a Majalisar Wakilai.

Ya shiga zauren majalisar ne a shekarar 2011 kuma ake damawa da shi har yanzu.

Dan majalisar ya yi aiki a kwamitoci da yawa, cikin har da na yaki da cin hanci da rashawa, da na hulda da jama’a da yada labarai, da kuma na harkokin da suka shafi kudi da bankuna.

Ba zai koma zauren majalisar ba saboda ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Neja a Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.