HomeLabaraiMbappe ne ya fi kowanne dan wasa daraja

Mbappe ne ya fi kowanne dan wasa daraja

Date:

Related stories

Gwamnatin Ribas ta soke amincewar amfani da filin wasanta wajen kamfen din Atiku

Gwamnatin jihar Ribas ta janye amincewarta na amfani da...

Babu wanda ya ke yakar Tinubu a fadar shugaban kasa, cewar gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba...

An kashe Fulani makiyaya 421 cikin watanni 3 a Najeriya – CPAN

Gamayyar kungiyoyin Fulani makiyaya ta Najeriya CPAN ta sanar...

‘Yan bindiga sun kai harin bam ofishin INEC

‘Yan  bindiga sun kaddamar da hari kan wani ofishin...

Majalisar dokokin Kano ta amince da daga darajar kwalejin Sa’adatu Rimi zuwa jami’a

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartas da kudurin dokar...

Shahararriyar mujallar nan ta Forbes ta wallafa cewar Kylian Mbappe shi ne dan wasan da yake kan gaba wajen samun kudin shiga mai tsoka a shekarar 2022 a duniya kuma karon farko bayan shekara tara da ba a samu ko dai Cristiano Ronaldo ko kuma Lionel Messi a matsayi na farko ba.

Forbes mai bincike da kididdigar kudi ta yi kiyasin cewar dan kwallon Paris St Germain da Faransa, mai shekara 23 ya samu $128m (£115.2m) a kakar nan sannan takwaran Mbappe a PSG, Lionel Messi shi ne na biyu da ya samu kudin shiga $120m (£108m) sai dan wasan Manchester United, Ronaldo na uku mai $100m (£90m).

Neymar da Mohamed Salah suna cikin biyar din farko kuma Neymar dan wasan PSG da tawagar Brazil , an kiyasta cewar ya samu $87m (£78.4m) a kakar 2022-23 shi kuwa dan kwallon Liberpool Salah da Masar ya hada $53m (£47.7m).

Wanda ya taba zama a mataki na baya ba daga tsakanin Ronaldo ko Messi ba, shi ne Dabid Beckham a 2013
Mbappe ya kai wannan matakin, bayan da ya saka hannu a PSG kan yarjejeniyar mai tsoka ta ci gaba da zama a kungiyar a watan Mayu a daidai lokacin an yi ta hasashen cewar Real Madrid zai koma.

Cikin jerin ‘yan wasan da Forbes ta bayyana Haaland da Mbappe sune ke kasa da shekara 30.

Jerin ‘yan wasan tamaula 10 da suka samu kudi mai tsoka a 2022 in ji Forbes
Kylian Mbappe PS Dala miliyan 128 (Fam miliyan 115.2) Lionel Messi PSG Dala miliyan 120m (£108m) Cristiano Ronaldo Manchester United Dala miliyan 100m (Fam miliyan 90)
Neymar PSG Dala miliyan 87 (Fam miliyan 78.4).

Mohamed Salah Liberpool Dala miliyan 53 (Fam miliyan 47.7).

Erling Haaland Manchester City Dala miliyan 39 (Fam miliyan 35.1) Robert Lewandowski Barcelona Dala miliyan 35 (Fam miliyan 31.5) Eden Hazard Real Madrid Dala miliyan 31m Fam 27.9m).

Andres Iniesta Bissel Kobe Dala miliyan 30m (Fam miliyan 27) Kebin de Bruyne Manchester City Dala miliyan 29 (Fam miliyan 26.1).

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories