Masari ya janye dokar hana hawa babur a Katsina

0
163

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin janye dokar hana hawa babura da gwamnatin ta kafa saboda matsalar tsaro.

Kafin dakatar da dokar dokar na fara aiki ne daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Gwamna Masari ya ce, janye dokar an yi ne domin masu hidimomin bukukuwan Mauludi da ake yi don tuna da ranar haihuwar fiyayyen halitta.

Janye dokar hana hawa babur din ya fara aiki ne tun daga wannan rana ta 14 ga watan Oktoba har zuwa 20 ga watan Nuwamba na 2022.